Isa ga babban shafi

'Yan Afirka na mutuwa saboda da yunwa - Majalisar Dinkin Duniya

Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyi masu zaman kansu sun yi gargadi kan yadda fatara da yunyi ke kara haddasa mutuwa ‘yan Afirka sakamakon fari da sauyin yanayi da rikice-rikice da ake samu a nahiyar.

Wata mata da yaran ta dake fama da yunwa sakamakon masifar 'yan Boko Haram.
Wata mata da yaran ta dake fama da yunwa sakamakon masifar 'yan Boko Haram. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Gargadin nasu shi ne na baya-bayan nan a jerin jan hankali da masu fafutuka da masana ke yi cewa Afirka na fuskantar matsalar karancin abinci da ba a taba ganin irinta ba cikin shekaru da dama.

Da suke shaidawa wani taron hadin guiwa na manema labarai a birnin Paris na kasar Faransa asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF da kungiyoyi masu zaman kansu Care da Oxfam suka ce akalla mutun guda na mutuwa a kowane dakika 36 saboda yunwa a kasashe irinsu Habasha, Kenya da Somaliya, yayin da Kusan mutane miliyan 20 a yankin Sahel ke fama da karancin abinci, in ji su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.