Isa ga babban shafi

MDD ta bukaci gaggauta tara kudin taimakawa kasashen Afrika 3 masu fama da yunwa

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci tattara kududaden taimakawa kasashen yankin kuryar gabashin Afrika da ke famada matsananciyar yunwa sakamakon farin da yankin ke fama da shi biyo bayan karancin ruwan sama na tsawon shekaru.

Tsananin yunwa na ci gaba da illa ga al'ummomin kasashen 3 na Habasha da Kenya da kuma Somalia.
Tsananin yunwa na ci gaba da illa ga al'ummomin kasashen 3 na Habasha da Kenya da kuma Somalia. ASSOCIATED PRESS - Mohamed Sheikh Nor
Talla

Majalisar ta ce mutane fiye miliyan 43 ne yanzu haka a kasashen Habasha da Somalia da kuma Kenya ke cikin tsananin bukatar agajin agajin gaggawa domin ceto su daga tagayyarar da suke ciki wanda ke kaiwa ga rasa rayuka.  

Hukumar da ke kula da ayyukan jin kai a majalisar OCHA ta ce, kusan mutane miliyan 24 daga cikin miliyan 43 da aka ambata, sun riga sun fada cikin bala’in yunwa a kasashen na Habasha da Kenya da kuma Somalia. 

Kasashen uku dai a yanzu haka na fuskantar bala’in fari mafi muni cikin shekaru 40, lamarin da ya janyo rashin saukar ruwan sama a wasu yankunansu saboda tasirin matsalar sauyin yanayi. 

Kididdiga dai ta nuna cewara kasar Somalia kadai, akalla mutane miliyan 6 da dubu 700 ke fama da karancin abinci, cikinsu kuma har da kananan yara fiye da dubu 500. 

Wannan hali da aka shiga ya sa babban sakataren majalisar dinkin duniya Antonio Guterres jagorantar taron kasashe a birnin New York da zummar tara dala biliyan 7 don tallafawa wadanda yunwar ta  tagayyyara a kasashen da ke yankin kuryar gabashin Afirka. 

Sai dai kawo yanzu kashi 20 cikin 100 na adadin tallafin da majalisar dinkin duniya ta nema kawai  aka iya tarawa. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.