Isa ga babban shafi

MDD ta nanata gargadi kan fuskantar matsananciyar yunwa a gabashin Afrika

Majalisar Dinkin Duniya ta sake nanata gargadi kan yiwuwar fuskantar matsananciyar yunwa a kasashen gabashin Afrika da suka kunshi Habasha da Kenya da kuma Somalia saboda hasashen fuskantar karancin ruwan sama.

Wasu iyalai a Somalia.
Wasu iyalai a Somalia. AP - Ben Curtis
Talla

Kasashen 3 na Somalia Kenya da Habasha yanzu haka na fama da matsananciyar matsalar yanayin da ba su taba gani ba cikin shekaru 40 da suka gabata, wanda ya karanci ruwan damuna da kuma rikicewa yanayin zuwan ruwan.

Hukumomin Majalisar dinkin duniya da suka kunshi na Abinci da na yanayi da na nom ana ci gaba da gargadi kan halin da kasashen 3 ka iya tsintar kansu nan da kankanin lokaci matukar aka gaza daukar matakan da suka dace.

A sanarwar hadaka da hukumomin 3 suka fitar sun ce yanayin zubar ruwan sama da kasashen suka saba gani daga watan mayu zai yi jinkiri har zuwa Oktoba da Disamba kafin zuba.

Sanarwar ta ce hasashen zubar ruwan hatta tsakanin watan na Oktoba zuwa Disamba zai zama mafi karanci da kasashen 3 suka taba gani.

A cewar sanarwar zuwa yanzu dabbobi miliyan 3 da dubu 600 suka mutu a kasashen Kenya da Habasha yankunan da kiwo ke matsayin babbar hanyar samun abinci yayinda kashi 3 na dabbobin Somalia suka mutu saboda wannan mummunan yanayi.

Haka zalika amfanin gona da tsirrai na na ci gaba da lalacewa tsawon lokaci dalili kenan da ya sanya miliyoyin mutane barin matsugunansu tare da kaura zuwa yankunan da ke da wadataaccen abinci da ruwan sha.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa yanzu haka mutane miliyan 16 da dubu 700 na fama da matsananciyar yunwa a kasashen 3 dai dai lokacin da farashin abinci ke ci gaba da tashi a wani yanayi da ba a taba gani ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.