Isa ga babban shafi

Amurka zata taimakawa kasashen Afirka 10 shawo kan matsalar yunwa

Kasar Amurka tace zata zuba Dala miliyan 215 a matsayin agajin gaggawa a wasu kasashen Afirka guda 10 domin shawo kan matsalar karancin abincin da suke fuskanta sakamakon illar sauyin yanayi da annobar korona da kuma yakin Ukraine.

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken tare da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres wajen taron samar da abinci
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken tare da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres wajen taron samar da abinci REUTERS - EDUARDO MUNOZ
Talla

Sakataren harkokin wajen kasar Antony Blinken ya sanar da haka lokacin da ya gana da wasu daga cikin takwarorin sa daga Afirka dake halartar taron karancin abinci na duniya a Birnin New York.

Kasashen da ake saran su amfana da agajin na Amurka sun hada da Algeria da Burkina Faso da Mauritania da Kamaru da kuma Najeriya.

Sauran sun hada da Kenya da Rwanda da Uganda da Tanzania da kuma Zimbabwe.

Sakatare Janar na Majalisar Dunkin Duniya Antonio Guterres yayi gargadin samun matsalar yunwa na dogon lokaci yayin da ya bukaci Rasha da ta bada damar fitar da hatsin dake kasar Ukraine domin samun sauki.

Guterres yace a cikin shekaru biyu kacal, mutanen dake fuskantar matsalar karancin abinci sun ninka daga miliyan 135 a duniya zuwa miliyan 276, yayin da sama da dubu 500 daga cikin su na fuskantar matsananciyar rayuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.