Isa ga babban shafi
Sauyin Yanayi

Abincinmu na ta'azzara matsalar sauyin yanayi - Masana

Binciken masana ya nuna cewa, abinci na da matukar tasiri a fafutukar yaki da matsalar sauyin yanayi kamar yadda wata kwararriya ta bankado bayan ta shafe shekaru 10 tana gudanar da nazari kan alakar da ke tsakanin abinci da dumamar yanayi.

Yadda hayaki mai gurbata muhalli ke fita.
Yadda hayaki mai gurbata muhalli ke fita. AP - Stefan Puchner
Talla

A wannan Alhamis din ne aka karrama kwararriyar a fannin kimiyya wato Cyntihia Rosenzweig, shugabar Sashen Nazari kan Tasirin Sauyin Yanayi a wata Cibiyar Binciken Sararin Samaniya saboda sabon binciken da ta gudanar.

A yayin zanta wa da Kamfanin Dillancin Labarai na AFP, masaniyar kimiyyar ta bayyana cewa, babu yadda za a shawo kan matsalar dumamar yanayi ba tare da mayar da hankali kan dakile gurbatacciyar iskar da ake fitarwa a yayin sarrafawa da kuma samar da  abincin da muke ci ba.

Ta kara da cewa, a wajen sarrafa abincin da muke ci ne, ake fitar da kashi daya bisa uku na daukacin gurbatacciyar iskar da dan Adam ke fitar da ita, tana mai cewa, dole a fara magance wannan matsalar kafin shawo kan sauyin yanayi a duniya.

Kazalika ta yi kashedin cewa, samar da tsaron abinci ga al’ummar duniya, ta ta’allaka da sauyin yanayi, kuma dole ne a tanadi wadataccen  abincin duk kuwa da irin matakan da za a dauka na yaki da dumamar yanayin a cikin shekaru 10 masu zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.