Isa ga babban shafi

Mutane miliyan 18 na fama da karancin abinci a gabashin Afrika

Wata kungiyar agaji mai zaman kanta da ake kira WaterAid, ta ce sama da mutane milyan 18 ne ke fuskantar matsalar karancin abinci, saboda farin da ake fama da shi a yankin Gabashin Afirka, kuma mata ne za su fi fuskantar ukubar sadaniyar wannan matsala a cewar kungiyar.

Mutanen gabashin Afrika kan yi tafiya mai nisa domin neman ruwan sha.
Mutanen gabashin Afrika kan yi tafiya mai nisa domin neman ruwan sha. AP - Mstyslav Chernov
Talla

A rahoton da ta fitar dangane da wannan matsala, WaterAid ta ce, mata kan yi tafiya mai nisa domin neman ruwan da za a yi amfani da su domin sha, girki da sauran bukatu na yau da kullum, lamarin da ke kara jefa matan cikin hadurra masu tarin yawa.

Daga cikin irin wadannan matsaloli har da fuskantar fyade da kuma kaurace wa zuwa makaranta domin samun ilimi, saboda yadda suke bata lokacinsu wajen neman ruwan a daidai lokacin da sauran ‘yan uwansu dalibai maza ke can suna daukar darasi.

Matsalar farin dai ta jefa kusan mutane milyan 18 da dubu 600 a yanayi na rashin abinci, lura da yadda shekaru da dama a jere, suna shuka amma ba tare da sun girbin abin da suke bukata ba, kuma wannan ita ce matsalar fari mafi muni tun baya ga wadda yankin ya fuskanta a farkon shekara ta 2000.

Olutayo Bankole-Bolawole, daraktar kungiyar ta WaterAid mai kula da Gabashin Afirka, ya ce, kasashen Habasa, Kenya da kuma Somalia ne suka fi fama da wannan matsala.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.