Isa ga babban shafi

Mutane miliyan 22 na cikin barazanar yunwa a gabashin Afrika

Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewar, akalla mutane miliyan 22 ke fuskantar barazanar tsananin yunwa a yankin gabashin Afirka sakamakon farin da ya mamaye yankin.

Mutane miliyan miliyan 22 ke fuskantar barazanar yunwa a kasashen yankin gabashin Afrika
Mutane miliyan miliyan 22 ke fuskantar barazanar yunwa a kasashen yankin gabashin Afrika REUTERS/African Union-United Nations
Talla

Kungiyoyin agaji sun ce,  tsawon shekarun da aka samu ba tare da isashen ruwan sama ba a kasashen Kenya da Somalia da kuma Habasha wanda sh ine mafi muni a cikin shekaru 40 ya taimaka gaya wajen zafafa matsalar.

Hukumomin sun ce, shekaru 4 kenan a jere ake fuskantar karancin ruwan sama, abin da ya yi sanadiyar mutuwar miliyoyin dabbobi da lalata amfanin gona da kuma tilasta wa mutane sama da miliyan guda da dubu 100 tserewa gidajensu domin neman abinci da ruwan sha.

Daraktan Hukumar Samar da abincin David Beasley ya ce, ya zama dole duniya ta gaggauta daukar mataki domin ceto rayukan wadannan mutane da farin ya fara yi wa illa.

Ko a farkon wannan shekara, hukumar samar da abincin ta yi gargadin cewar mutane miliyan 13 ke fuskantar barazanar yunwa a wadannan kasashe guda 3.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.