Isa ga babban shafi

Yankin Somaliland ya janye daga tattaunawar hadewa da Somalia

Gwamnatin yankin Somaliland ta janye daga shirin tattaunawarta da Somalia, bayan kalaman da shugaban Uganda Yuweri Museveni ya yi a matsayin sa na mai shiga tsakani.

Taswirar Somaliland
Taswirar Somaliland © RFI
Talla

Tun farko an shirya tattaunawa da kasashen ne don kawo karshen rikicin da ke yawan ta shi a tsakanin su, tattaunawar da shugaban Uganda Museveni zai jagoranta.

To sai dai jim kadan kafin tattaunawar, Somaliland ta janye, inda ta ce sam kalaman da shugaba Yuweri ya yi, ba su yi dai-dai da tsarin ta ba.

Ya yin tattaunawarsa da manema labarai, Museveni ya ce a lokacin tattaunawar zai yi iya bakin kokarinsa wajen ganin kasashen sun sake hadewa bayan rabuwar su a 1991.

Gwamnatin ta Somaliland ta ce ba za ta shiga kowacce irin tattaunawa da Somalia akan batun sake hadewar su, abinda za ta saurara yayin tattaunawar kadai shine yadda za a ci gaba da tafiya cikin kwanciyar hankali amma kowacce kasa na cin gashin kanta.  

Tun 1991 da Somaliland ta ayyana ballewa daga Somalia, sai dai har kawo yanzu ba ta sami amincewa daga kasashen duniya ba.

Tun bayan ficewar Somaliland daga Somalia ne kuma wani sabon rikici ya sake ballewa, inda wasu shugabannin gargajiya da ke garuruwan kan iyakokin kasar ke bukatar sake samar da wata kasa da suke kira da Puntland a maimakon kasancewar su cikin Somaliland.

Yunkurin samar da kasar ta Puntland ya lakume rayukan mutane fiye da 300, sai wasu mutane dubu 1,913 da suka jikkata ya yin da fiye da mutane 200,000 suka bar muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.