Isa ga babban shafi

Wani sabon rikici a Somaliland ya kashe mutane 34

Akalla mutane 34 suka mutu a wani sabon rikici da ya barke a arewacin yankin Somaliland a jiya litinin rikcin da tuni majiyoyin lafiya daga garin Laascaanood suka tabbatar da faruwarsa. 

Wani yanki a Somaliland.
Wani yanki a Somaliland. N Williams/Save the Children
Talla

A cewar ministan kula da harkokin cikin gida na yankin, rikicin ya barke ne da safiyar litinin, tsakanin sojojin yankin da ya bayyana cin gashin kan sa a shekarar 1991, da kuma masu adawa da gwamnati. 

Yankin na Somaliland dai bai samu goyon baya yadda ya kamata daga kasashen ketare dangane da ‘yancin sa ba, kuma yana fuskantar masu adawa musamman daga gabashin iyakar sa da Puntland da suka fice daga Somalia. 

Wani likita a asabitin garin Laascaanood Mohamed Farah, ya ce mutane 34 suka mutu sannnan wasu 40 suka raunata. 

Shugaban yankin na Somaliland Muse Bihi, ya yi gargadin cewa a shirye suke su kare martabar ‘yancin kasar su. 

Yankin na Somaliland dai na da zaman lafiya fiye da kasar Somalia da ya balle daga ciki, in banda a ‘yan watannin baya-bayan nan daya fara fuskantar zanga-zanagar siyasa da ke kokarin kawo barazana ga zaman lafiyar sa. 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.