Isa ga babban shafi

Ana taron tattaunawa kan murkushe Al-Shebaab a Somalia

An tsaurara matakan tsaro a birnin Mogadishu na Somalia a daidai lokacin da ake shirin gudanar da wani taro a ranar Laraba kan yadda za a murkushe mayakan Al-Shebaab.

Mayakan Al-Shebaab a shekarar 2011
Mayakan Al-Shebaab a shekarar 2011 AP - Farah Abdi Warsameh
Talla

Shugabannin kasashen gabashin Afrika da suka kafa rundunar yaki da ‘yan ta’adda, za su halarci wannan taro don tattaunawar keke da keke kan barazanar da kasashensu ke fuskanta daga mayakan na Al-shebaab.

Gwamnatin Somalia ta ce, ana sa ran taron zai gaggauta daukar matakin ceto kasar daga wadannan kawarijawa, wato kalmar da gwamnatin ke amfani da ita wajen kiran Al-Shebaab.

Sojojin kasar gami da mayakan sa-kai masu samun goyon baya daga sojojin Kungiyar Kasashen Afrika ta AU da ake kira ATMIS, sun kaddamar da jerin hare-hare kan mayakan na Al-Shebaab a watannin baya-bayan nan, abin da ya ba su damar sake karbe iko da wasu yankuna da mayakan suka mamaye a can baya.

Jim kadan da shan rantsuwar kama-aiki a cikin watan Mayun bara, shugaban kasar ta Somalia, Hassan Sheikh Mohd.ya ayyana yakin taron-dangi kan mayakan masu alaka da Al-Qaeda.

Al-Shebaab ta shafe fiye da shekaru 15 tana addabar Somalia, yayin da sojojin AU suka yi nasarar fatattakar ta daga babban birnin Mogadishu a shekarar 2011, amma har yanzu tana ci gaba da rike wasu yankuna na bayan-gari, inda daga nan ne take kitsa kaddamar da hare-hare a cikin kasar da ma makotanta.   

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.