Somalia: Wani abu ya fashe a kusa da ofishin magaajin garin Mogadishu
Fashewar wani abu kusa da ofishin magajin garin Mogadishu a tsakiyar birnin ya lalata gine gine a Lahadin nan, inda daga bisani aka kaure da musayar wuta a tsakanin dakarun gwamnatin Somalia da na kungiyar Al-Shabaab, wadda tuni ta dau alhakin harin.
Wallafawa ranar:
Wani babban jami’in ‘yan sanda a birnin, Abdullahi Mohamed ya ce ‘yan ta’addan sun yi amfani da wata mota ce da suka makare da abubuwa masu fashewa wajen kai harin.
Ganau sun ce fashewar ta lalata gine ginen da ke kusa da wurin, kuma har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, ana iya jin karar musayar wuta daf da ofishin magajin garin na birnin Mogadishu.
Sun ce an samu wadanda abin ya rutsa da su, amma jami’an tsaron sun yi wa yankin kawanya, tare da umurnin cewa kowa ya bar wurin.
Kungiyar Al-Shabaab, mai alaka da Al-Qaeda ta dau alhakin wannan harin ta wata tashar sadarwarta, tana mai cewa mayakanta sun kutsa cikin ginin da suka kai harin bayan da suka kasha masu gadi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu