Isa ga babban shafi

Rikici ya tilasta wa 'yan Somaliland dubu 100 tserewa zuwa Habasha

Wasu alkaluman Majalisar Dinkin Duniya sun nuna yadda rikici ya tilastawa mutane fiye da dubu 100 tserewa daga yankin Somaliland zuwa kudancin Habasha da ke fama da matsanancin fari mafi muni a tarihi.

Wani Yanki a Somaliland.
Wani Yanki a Somaliland. N Williams/Save the Children
Talla

Alkaluman da hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya da takwararta ta Habasha suka fitar sun ce yankin Doolo da ke kudu maso gabashin kasar mai tazarar kilomita dubu 1 da 300, ya yi rijistar ‘yan gudun hijira fiye da dubu 98 wadanda suka fara kwararowa daga yankin Somaliland tun a ranar 6 ga watan Fabarairun da ya gabata.

Babban daraktan hukumar kula da ‘yan gudun hijrar ta Habasha Tesfahun Gobezay ya ce tuni aka bayar da matsugunan wucin gadi ga mutanen wadanda yaki ya koro daga yankinsu na Somaliland wanda ya balle daga Somalia tare da ayyana kansa a matsayin mai cikakken ‘yanci.

Sai dai Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi kan halin da ‘yan gudun hijirar za su shiga lura da yanda suka yada zango a yankin na Doolo da ke sahun yankunan masu fama da matsanancin fari na tsawon shekaru 4 a kasar ta Habasha.

A cewar hukumar ta UNHCR tun gabanin isar jami’ansu tuni al’ummar yankin suka fara bayar da matsugunai ga ‘yan gudun hijirar wadanda ke ci gaba da kwararowa dai dai lokacin da rikicin ke ci gaba da karfi a yankin na Somaliland.

Wani babban jami’I a hukumar Mamadou Dian Balde ya ce adadin ‘yan gudun hijirar na ci gaba da yawaita a kowacce rana wanda zai kara matsalar da yankin mai yawan jama’a dubu 236 ke fuskanta na yunwar da tuni ta jefa al’ummar yankin a matsanancin hali.

Yankin na Somaliland wanda Birtaniya ta yiwa mulkin malla a shekarar 1991 ne ya balle daga Somalia kuma tun daga wancan lokaci bai hadu da gagarumin rikici ba sai a yanzu da wasu yankuna suka sanar da shirin komawa don hadewa da Somalia lamarin da ya haddasa rikici.

Habasha mai yawan jama’a miliyan 120 yanzu haka na karbar ‘yan gudun hijira dubu 880 galibinsu daga kasashen Sudan ta kudu da Sudan da Somalia da kuma Eritrea.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.