Isa ga babban shafi

Kasashe sun bukaci tsagaita wuta a Somaliland bayan bukatar Lascanood ta hadewa da Somalia

Manyan kasashe sun fara bayyana damuwa kan karuwar tashe-tashen hankula a yankin Somaliland wanda ke ci gaba da tsananta tun daga karshen shekarar da ta gabata, inda zuwa yanzu rayukan tarin fararen hula ya salwanta.

Wani yanki a Somaliland.
Wani yanki a Somaliland. AFP - EDUARDO SOTERAS
Talla

Kasashen Qatar da Somalia da Turkiya da hadaddiyar daular larabawa baya ga Birtaniya da Amurka dukkaninsu sun aike da sakon bukatar zaman lafiya a yankin bayan rikicin farkon watan jiya da ya kashe mutane 34.

Kasashen 6 a wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar sun nemi tsagaita wuta a rikicin bangarorin biyu da ke yankin Lascanood, tare da bayar da damar shigar da kayakin agaji don taimakawa wadanda rikicin ya daidaita.

Tuni dai mahukuntan yankin suka sanar da jibge jami’an tsaro a Lascanood inda rikicin ya faro a bara yankin da ke matsayin cibiyar kasuwancin Somaliland.

A farkon watan fabarairun da ya gabata ne, fada ya dawo sabo a Somaliland bayan da lardin Sool da Lascanood ke ciki ya bayyana aniyar komawa ya hade da kasar Somalia.

Somaliland wanda ya balle daga Somalia a shekarar 1991 na da yawan jama’a miliyan 4 da rabi dukkanin a yankuna 3, na cikin zaman lafiya tun bayan ballewarsa gabanin yunkurin na Lascanood a karshen shekarar da ta gabata, inda mahukunta yankin suka aike da sakon goyon baya ga gwamnatin Somalia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.