Hadaddiyar Daular Larabawa ta dauki nauyin ginawa Afirka ta Tsakiya sabon filin jirgi na zamani
A jamhuriyar Tsakiyar Afrika,wata tawagar kungiyar kasashen Brics da ta ziyarci wannan kasa ta cimma yarjejeniya da hukumomin kasar na sake fasalta wasu daga cikin manyan ayuka da suka jibanci sufuri,sadarwa.
Wallafawa ranar:
Ministan Sufuri Afrika ta Tsakiya, Herbert Gontran Djono Ahaba, da Shugaban kasar Faustin Archange Touadéra, sun bayyana farin cikin su ganin ta yada aka cimma yarjejeniya na gina sabon filin jirgin sama a babban birnin Bangui, aikin da Hadaddiyar Daular Larabawa ta dauki nauyin sa.
Hukumomin na Afirka ta Tsakiya zasu samar da fili mai fadin hekta dari uku domin gina wannan sabon filin jirgin a wajen Bangui, yayinda ake bayyana cewa Masarautar daular Larabawa za ta ware kudi zuzzurutu dalar Amurka miliyan 200, sama da CFA biliyan 120 dangane da wannan aiki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu