Isa ga babban shafi

Bayan mutuwar Prigozhin, mecece makomar kamfanin Wagner a Afirka?

Kasashe da dama ne za su tuna da wanzuwar Yevgeny Prigozhin, da kuma dalilai daban-daban. A Kiev, saboda jagorantar mayakansa zuwa fagen daga a Ukraine, a Rasha, a matsayin dan kishin kasa kuma a matsayin mayaudari ga yunkurinsa yin tawaye ga fadar gwamnatin Moscow a watan Yuni.

Yadda masu alhini ke sanya furanni a gaban kamfanin Wagner na kasar Rasha, bayan tabbatar da mutuwar Yevgeny Prigozhin.
Yadda masu alhini ke sanya furanni a gaban kamfanin Wagner na kasar Rasha, bayan tabbatar da mutuwar Yevgeny Prigozhin. AFP - STRINGER
Talla

Har ila yau, za a iya tunawa da Prigozhin a kasashe masu nisa da Rasha, kamar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Mali, inda gwamnatocin kasashen ke dogaro da ayyukan kungiyarsa ta Wagner domin dakile barazanar tsaro.

Kazalika, ra'ayin jama'a a wadannan kasashe na kallon Wagner da gwamnatin Rasha a matsayin abokan hulda ne da ke taimakawa kasashensu su maido da ikonsu daga Faransa.

An tabbatar da kasancewar kwangilar kamfanin Wagner a Afirka a shekarar 2018 a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya bayan da Shugaba Faustin Archange Touadera ya nemi taimakonm sojojin hayar don murkushe 'yan tawaye.

Tuni dai Rasha ta taimaka wajen sake gina sojojin kasar tare da tabbatar da tsaron babban birnin Bangui.

A kasar Mali, sojojin da ke mulkin kasar sun garzaya zuwa birnin Moscow domin neman mafita ta yadda za a dakile hare-haren 'yan ta'adda, amma kuma ana ganin domin kawar da sojojin Faransa ne.

Ba a dau lokaci mai tsawo ba sai makwabciyarta Burkina Faso, da ke fama da tashe-tashen hankulan masu dauke da makamai da suka haifar da kwace mulkin kasar da sojoji suka yi, ta nemi agaji.

A Afirka, kamfanin Wagner ya ci gaba da cika burin Moscow na soja, siyasa da tattalin arziki, abin da ya fusata shugabannin yammacin duniya wadanda ke nuna rashin jin dadi.

A jamhuriyar Nijar, kasar yankin Sahel ta baya-bayan nan da ta fuskanci juyin mulki, masu goyon bayan gwamnatin mulkin soji sun bukaci Rasha ta shiga tsakani, kuma ana sa ran ficewar sojojin Faransa daga kasar.

Tambayoyi game da makomar ayyukan Wagner a Afirka sun yi yawa tun lokacin da Prigozhin ya yi tawaye ga gwamnatin Moscow a watan Yuni, sa'an nan, ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta ce abubuwan da suka faru ba za su yi wani tasiri ba kan ayyukan kungiyar.

Duk da yake mutuwar Prigozhin babu shakka ta zo lokacin da ake ganin Rasha na amfani da shi wajen cimma wasu manufofi, abin tambayar shine, ko yaya makomar Wagner za ta kasance, musamman a kasashen da ya fara tasiri?

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.