Rasha ta ce Ukraine ta kai mata hari da jirage marasa matuki sau 6 a jere
Mahukunta a Rasha sun ce, wani jirgi mara matuki na Ukraine ya kai hari kan wani gini a Cibiyar Kasuwanci na birnin Moscow. Karo na 6 kenan a jere da makamantan jiragen ke kai hare-hare cikin dare a babban birnin Rasha a cewarsu.
Wallafawa ranar:
Wannan harin na baya-bayan nan a kan Moscow na zuwa ne bayan da mahukuntan Ukraine suka ce Rasha ta yi amfani da manyan makaman atilari wajen kai hare-hare a wasu kauyukanta biyu a kusa da birnin Lyman na iyakar Ukraine da Rasha ta gabashin kasar, abin da ya yi sanadin mutuwar mutane uku tare da jikkata wasu biyu.
Yankin Moscow, wanda ke da nisan daruruwan kilomita daga filin-daga ya fuskanci hare-hare babu kaukautawa a cikin makwannin baya-bayan nan, sai dai babu wani rahoton mummunar barna.
A wata sanarwa, Ma’aikatar Tsaron Rasha ta ce ta kakkabo wani jirgi mara matuki a gundumar Mozhaisky da karin wani a gundumar Khimki na yankin Moscow.
Rasha da Ukraine sun yi ta bai wa hammata iska tun daga farkon wannan mamaya da shugaba Vladimir Putin ya sahale tun a shekarar da ta gabata, a yayin da yanzu aka kai gabar da dakarun Ukraine ke kara azama a martanin da suke mayarwa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu