Isa ga babban shafi

Ana fargabar mutuwar shugaban sojin haya na Rasha

Shugaban sojojin haya na Rasha, Yevgeny Prigozhin na cikin fasinjojin jirgin saman da ya yi hatsari a wannan Larabar, kuma akwai yiwuwar ya mutu.

Shugaban sojojin haya na Wagner, Yevgeny Prigozhin a wani yanki na Sahel a Afrika a cikin wannan makon.
Shugaban sojojin haya na Wagner, Yevgeny Prigozhin a wani yanki na Sahel a Afrika a cikin wannan makon. via REUTERS - PMC WAGNER
Talla

 

Kamfanin Dillancin Labaran Kasar mallakin gwamnati ne ya rawaito haka a wannan yammaci, yana mai cewa, hatsarin jirgin ya auku ne a yankin Tver mai tazarar kilomita 60 daga babban birnin Moscow, kuma Prigozhin na cikin jerin fasinjojin.

Tuni Kamfanin Sojin Hayar na Wagner ya yi zargin cewa, sojojin Rasha masu tsaron sararin samaniya ne suka kakkabo jirgin da Prigozhin ke ciki.

Prigozhin shi ne wanda ya jagoranci wasu sojoji suka yi wa gwamnatin shugaba Vladimir Putin tawaye a cikin watan Yunin da ya gabata, lamarin da ya dauki hankula a ciki da wajen Rasha.

A wancan lokacin, shugaba Putin ya bayyana shi a matsayin maciyin amanar kasa kafin daga bisani suka cimma wata yarjejeniya da ta tilasta masa yin gudun hijira zuwa Belarus.

A cikin wannan makon ne, wani faifen bidiyo ya nuna Prigozhin tsaye da zungureriyar bindiga a wani yanki na Sahel a nahiyar Afrika, a daidai lokacin da Wagner ta fara daukar sojoji daga nahiyar ta Afrika  a cewar rahotanni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.