Isa ga babban shafi

Kamfanin sojojin haya na Amurka ya fara tattaunawa da Afrika ta tsakiya don kulla alakar tsaro

Kamfanin sojojin haya na Amurka Bancroft Global development ya fara tattaunawa da gwamnatin Africa ta tsakiya don kulla alakar tabbatar da tsaro, dai-dai lokacin da kasashen turai musamman Amurkan ke adawa da kasancewar sojojin haya na Wagner a nahiyar Africa.

Har yanzu dai gwamnatin kasar bata ce komai kan wannan lamari a hukumance ba
Har yanzu dai gwamnatin kasar bata ce komai kan wannan lamari a hukumance ba AP - Alexander Ryumin
Talla

 

Tuni dai masu fashin baki suka fara zargin wannan kamfani da alaka ta kai tsaye da gwamnati, kuma an samar da shi don zama kishiya ga Wagner, wanda a yanzu mafi yawancin kasashen Africa suka fi aminta da shi fiye da sojojin kasashen yammacin duniya.

Tun watanni da suka gabata ne aka fara zargin gwamnatin da kulla alaka da kamfanin na Bancroft, kuma har ya aike da sojojin sa, sai dai kamfanin ya musanta haka, amma ya ce ya fara tattaunawa da shugaba Faustin Archange Touadera.

Kamfanin wanda aka kafa shi a farkon watan Yulin da ya gabata na da manufar taimakawa kasashe musamman na Africa wajen yaki da ‘yan ta’adda da sauran kungiyoyi masu rike da makamai.

Sai dai wata majiya ta kusa da shugaban kasar a Bangui ta shaidawa sashen Ingilishi na RFI cewa tuni sojojin suka isa kasar amma basu fara aiki ba, ikirarin da kamfanin ya musanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.