Isa ga babban shafi

Daruruwan dakarun Wagner sun isa Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya

Daruruwan dakarun kamfanin tsaro na Wagner sun isa kasar Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, domin tabbatar da tsaro gabanin zaben jin ra’ayoyin jama’a da za’a yi a ranar 30 ga wannan watan na Yuli, kamar yadda kamfanin ya sanar.

Wasu daga cikin dakarun kamfanin ba da sojojin haya na Wagner a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.
Wasu daga cikin dakarun kamfanin ba da sojojin haya na Wagner a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. © Franceinfo
Talla

A cewar sanarwar da kamfanin sojojin hayan ya fitar, jami’ansa da ke bada horo na ci gaba da horas da jami’an tsaron kasar Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, don inganta sha’anin tsaron kasar gabanin zaben.

A farkon wannan watan ne dai wasu majiyoyi suka bayyana cewar sojojin Wagner na ficewa daga kasar, batun da tuni gwamnatin kasar ta musanta.

Tun bayan boren da sojojin Wagner suka yi a ranakun 23 zuwa 24 ga watan da ya gabata a Rasha, aka fara sanya alamar tambaya gameda makomar ayyukansa a wasu kasashe.

Toh sai dai har yanzu Wagner na ci gaba da gudanar da ayyuka a kasashen Syria da Sudan da Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya da Mali, inda ma bayan boren Bangui ya sake tabbatar da ci gaba da ayyukan Wagner a cikinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.