Isa ga babban shafi

An soma zaben shugaban kasa a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya

An soma zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa a Afrika ta Tsakiya, inda shugaba mai ci Faustin Archange Touadera ke neman wa’adi na 2.

An soma zaben shugaban kasada na 'yan majalisa a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya
An soma zaben shugaban kasada na 'yan majalisa a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya Centre for Humanitarian Dialogue
Talla

Zaben dai yazo ne a yayin da sojojin kasar ke cigaba da fafatawa da ‘yan tawaye da suka sha alwashin hana gudanarsa, bayan janye shelar tsagaita wutar da suka yi, gami da kudurar aniyar kame Bangui, babban birnin kasar.

A ranar Asabar Majalisar Dinkin Duniya tace ‘yan tawayen sun halaka dakarunta 3 dake aikin wanzar da zaman lafiya a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiyan.

Sanarwar ma’aikatan tsaron tace masu tayar da katayr bayan sun kaddamar da farmaki kan hadin gwiwar dakarun sojin ne a garuruwan Dekoa da Bakouma dake yankunan Kemo da kuma Mbomou a kudancin kasar.

Gabannin zaben na yau, sai da shugaba Touadera ya zargi tsohon shugaba Francois Bozize da yunkurin kifar da gwamnati, tuhumar da yayi watsi da ita.

A makon jiya kotu daukaka kara a Afrika ta Tsakiyan tayi watsi da bukatar tsohon shugaba Bozize, dake neman soki hukuncin haramta mishi takara, sakamakon takunkumin da majalisar dinkin duniya ta kakaba masa, bisa tuhumarsa da aikata laifukan yaki a zamanin da yake mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.