Isa ga babban shafi
Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya

'Yan tawayen Afrika ta tsakiya sun janye bukatar tsagaita wuta

Babbar kungiyar ‘yan tawayen Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya da ke fada da gwamnatin kasar ta sanar da janye tsagaita wutar da ta bukata na kwanaki 3 gabanin zaben kasar da ke zuwa ranar Lahadi.

Wasu 'yan tawayen Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya.
Wasu 'yan tawayen Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya. Reuters
Talla

Wata sanarwa da hadakar kungiyoyin masu fada da gwamnatin ta Afrika ta tsakiya suka fitar ta ce ta dauki matakin janye tsagaita wutar daga bangarenta ne na sa’o’i 72 ta yadda za ta ci gaba da kalubalantar gwamnati har zuwa cikar kudirin da ta sanya a gaba.

Sanarwar wadda kungiyoyi 2 cikin 6 da ke cikin hadakar suka mikawa kamfanin dillancin labaran Faransa, ta ce sun dauki matakin ne don kalubalantar yunkurin gwamnati.

Takardar janye tsagaita wutar wadda te nemi hukumomin kasar ta Afrika ta tsakiya su aminta da ita, ta kuma bukaci shugaban kasar Faustin Archange Touadera ya gaggauta dakatar da zaben na Lahadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.