Isa ga babban shafi
Rwanda

Rwanda ta aike da dakarunta Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya

Rwanda ta aike da daruruwan dakarunta zuwa Jamhuriyar Tsakiya Afrika, inda ake kai farmaki kan sojojinta da ke aiki a rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, kamar yadda ma’aikatar tsaron kasar ta bayyana a wata sanarwa.

Paul Kagame, shugaban Rwanda.
Paul Kagame, shugaban Rwanda. SIA KAMBOU / AFP
Talla

Sanarwar da ta fito daga ma’aikatar tsaron Rwanda ta ce wannan mataki na zuwa ne a matsayin martani ga hare haren da dakarun ‘yan tawaye masu biyayya da tsohon shugaban kasar Francois Bozize ke kaiwa sojojinta.

A ranar Asabar ne gwamnatin Jamhuriyar Tsakiyar Afrika ta zargi Bozize da kokarin jagorancin juyin mulki, a yayin da hankula ke ci gaba da tashi gabaninn zaben shugaban kasar da zai gudana ranar Lahadi.

Rundunar kiyaye zaman lafiya ta majalisar dinkin Duniya ta ce ‘yan tawaye masu dauke da makamai sun fara kutsawa babban birnin kasar Bangui, amma kuma dakarunta sun maida su baya.

Babu cikakken bayani a kan adadin dakarun da Rwanda za ta tura, ko kuma ran da za ta aike da su, amma ma’aikatar tsaron kasar ta ce za ta kuma taimaka wajen tabbatar da an yi zaben na Lahadi mai zuwa cikin kwanciyar hankali a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.