Isa ga babban shafi
Faransa-Rwanda

Faransa na bincike kan tsohon shugaban sashin leken asirin sojin Rwanda

Gwamnatin Faransa ta soma bincike kan zarge-zargen da ake yiwa tsohon shugaban sashin leken asirin rundunar sojin Rwanda, Aloys Ntiwiragabo na cin zarafin dan adam, yayin kisan kare dangin da aka yiwa dubban ‘yan kabilar Tutsi a shekarar 1994.

Hotunan wasu daga cikin dubban mutanen da aka yi wa kisan gilla a Rwanda.
Hotunan wasu daga cikin dubban mutanen da aka yi wa kisan gilla a Rwanda. © Baz Ratner/REUTERS
Talla

Jami’an hukumar binciken laifukan ta’adanci a Faransa sun kaddamar da binciken ne kwana guda bayan bankado maboyar Ntiwiragabo tare da kame shi a Orleans dake kudu maso yammacin Faransa.

Tuni dai kotun sauraron shari’ar kisan kare dangin da ka yi a Rwanda da majalisar dinkin duniya ke marawa baya, ta bayyana tsohon shugaban leken sirin sojin a matsayin daya daga cikin wadanda suka shirya kisan gillar da aka yiwa mutane dubu 800 a 1994, mafi akasarinsu ‘yan kabilar Tutsi.

Manyan masu laifukan da ake zargi da take hakkin dan adam ko kisan kare dangi da ake nema ruwa a jallo, sun dade suna buya a Faransa.

Watanni biyu da suka gabata ne kuma, jami’an tsaron kasar suka kame Felicien Kabuga, attajirin da ake tuhuma da bada kudaden sayen makaman da aka yi amfani da su, wajen aikata kisan kare dangin na 1994 a Rwanda.

Kabuga ya shiga hannu ne bayan shafe shekaru 25 yana wasan buya da jami’an tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.