Isa ga babban shafi
Rwanda

Kisan Rwanda:Kabuga ya shiga hannun kotu a Afrika

Wata kotun daukaka kara da ke birnin Paris ta ce, mutumin da ake zargi da zama kanwa uwar gami a kisan kiyashin kasar Rwanda, Felicien Kabuga, da aka kama shi a Faransa bayan farautar sa tsawon shekaru 25, an mika shi ga kotun kasa da kasa da ke Tanzania domin fuskantar shari'a.

An shafe tsawon shekaru ana farautar Kabuga
An shafe tsawon shekaru ana farautar Kabuga Reuters
Talla

Kabuga dai shi ake zargi da daukar nauyin amfani da dukiyarsa wajen kisan kiyashin shekara ta 1994, inda rayukan mutane dubu 800 suka salwanta, wanda a yanzu yake bukatar a yi masa shari'a a Faransa saboda a cewarsa, ba shi da koshin lafiya, sannan kuma wai kotu a Afrika ba za ta yi masa adalci ba don ana iya mika shi ga Hukumomin Rwanda.

Yanzu haka dai batunsa na da sauran mataki kafin a san inda aka dosa, kasancewar lauyoyinsa na shirin daukaka kara a kotun Faransa.

A kan keken guragu ne dai aka kai Kabuga mai shekaru 84 gaban kotu a jiya Laraba.

Kabuga ya buya a Faransa  shekara da shekaru da sunan karya, inda yake amsa sunan Antonie Tounga.

‘Ya'yansa ne ke kulawa da shi duk tsawon shekarun nan da ya yi yana wasan buya da jamian tsaro, amman kuma daga bisani ‘yan sandan Faransa da  Belgiun da Britaniya sun yi amfani da ‘ya’yan nasa ne suka yi nasarar kama shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.