Isa ga babban shafi
Rwanda

Rwanda ta aike da karin dakaru Jamhuriyar Afrika ta tsakiya gabanin zabe

Ma'aikatar tsaron Rwanda ta ce kasar ta aike da karin dakaru Jamhuriyyar Afrirka ta tsakiya, sakamakon tsanantar hare-hare kan Sojin da ke aikin wanzar da zaman lafiya karkashin shirin Majalisar Dinkin Duniya.

Wasu dakarun Sojan Rwanda.
Wasu dakarun Sojan Rwanda. AFP PHOTO / JUNIOR D. KANNAH
Talla

Sanarwar da ta fito daga ma’aikatar tsaron Rwanda ta ce wannan mataki na zuwa ne a matsayin martani ga hare-haren da dakarun ‘yan tawaye masu biyayya da tsohon shugaban kasar Francois Bozize ke kai wa sojojinta.

A ranar Asabar ne gwamnatin Jamhuriyar Afrika ta tsakiyar ta zargi Bozize da kokarin jagorancin juyin mulki, a yayin da hankula ke ci gaba da tashi gabanin zaben shugaban kasar da zai gudana ranar Lahadi.

Rundunar kiyaye zaman lafiya ta majalisar dinkin Duniya ta ce ‘yan tawaye masu dauke da makamai sun fara kutsawa babban birnin kasar Bangui, ko da ya ke dakarunta sun maida su baya.

Babu cikakken bayani a kan adadin dakarun da Rwanda ta tura, ko kuma ran da za ta aike da su, amma ma’aikatar tsaron kasar ta ce za ta kuma taimaka wajen tabbatar da an yi zaben na Lahadi mai zuwa cikin kwanciyar hankali a kasar.

Sanarwar ma’aikatar tsaron na Rwanda ta ce da ita da Rasha ne suka tura daruruwan dakaru zuwa Afrika ta Tsakiyar, sai dai babu tabbaci daga Rasha a game da haka, amma Rashan ta sha nanata cewa akwai takaici a game da abin da ke faruwa a Jamhuriyyar Afrika ta Tsakiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.