Isa ga babban shafi

An tsare shugaban Otel Rwanda mai adawa da Kagame

Yan sandan kasar Rwanda sun gabatar da Tsohon shugaban Hotel Mille Collines, Paul Rusesabagina a gaban kotun Kigali, inda aka zarge shi assasawa da daukar nauyin tafiyar da kungiyar 'yan tawayen kasar, bugu da kari an kuma zargeshi da yin garkuwa tare da aikata kisan kai.

Shugaban Otel na Rwanda kuma dan adawar kasar Paul Rusesabagina
Shugaban Otel na Rwanda kuma dan adawar kasar Paul Rusesabagina NICOLAS MAETERLINCK / BELGA / AFP
Talla

Paul Rusesabagina, shine shugaban Hotel din da ya ceci dubban 'yan kabilar Tutsis da Hutus a lokacin kisan kiyashin kasar, al’amarin da ya kai masana'antar shirya fina finan kasar Amruka ta Hollywood ta shirya film a kan labarin mai suna "Hotel Rwanda".

A shekarar 1994. Tun lokacin ne tsohon shugaban hotel din ya zama rikakken dan adawa ga gwamnatin Kigali shekaru sama da 15 da suka gabata, inda da farko ya kirkiri jamíyar adawa mai suna PDR (Parti démocratique rwandais) a lokacin da yake zaman gudun hijira.

Tuni dai aka zargi Paul Rusesabagina da taimakawa kungiyar yan tawayen kasar Rwanda da kudade zargin da ya musanta.

Yanzu haka dai shugaban kasar ta Rwanda Paul Kagame na kan waádin mulki na 3 ne, al’amarin da yan adawa da dama ke ganin gwagwarmayar makamai kawai zata bada damar kawar da shugaban na Kigali daga kan mulki.

A lokacin da aka kafa kungiyar siyasa da makamai ta MRCD a watan yulin 2018, an gabatar da Paul Rusesabagina a matsayin mataimakin kungiyar reshen siyasa bayan canza mata suna da FLN.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.