Isa ga babban shafi
Rwanda

Belgium ta kama masu hannu a kisan Rwanda

Hukumomin Belgium sun cafke mutane uku tare da tuhumar su kan zargin su da hannu a kisan kare dangin da ya auku a shekarar 1994 a Rwanda.

Akalla mutane dubu 800 suka mutu a rikicin Rwanda na shekarar 1994
Akalla mutane dubu 800 suka mutu a rikicin Rwanda na shekarar 1994 REUTERS/Jean Bizimana
Talla

Ofishin Mai Shigar da Kara na Gwamnatin Belgium da ya fitar da sanarwar, bai yi karin haske ba game da wadannan mutane uku, amma an gano su tare da taimakon wata shaida da masu bincike suka tattaro daga Rwanda.

Tuni aka tuhumi mutanen uku kan keta hakkin dan adam kamar yadda mai magana da yawun ofishin mai shigar da karar na Belgium ya bayyana.

Akalla mutane dubu 800 suka rasa rayukansu a kisan kare dangin na Rwanda, kuma akasarinsu sun fito ne daga kabilar Tutsi.

A ranar Talata ce aka cafke biyu daga cikinsu, yayin da a ranar Laraba aka damke cikon na ukun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.