Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya

'Yan tawayen Afrika ta Tsakiya sun yi shelar tsagaita wuta saboda zabe

Wasu kungiyoyin ‘yan tawaye da suka hada gwiwa wajen yakar gwamnatin Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, sun yi shelar tsagaita wuta don bada damar gudanar da zabukan kasar cikin kwanciyar hankali a ranar Lahadin dake tafe.

Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya
Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya ALEXIS HUGUET / AFP
Talla

Sanarwar da gamayyar kungiyoyin ‘yan tawayen 6 suka fitar ta ce yarjejeniyar tsagaita wutar za ta shafe sa’o’i 72 tana aiki.

Kusan mako guda kenan da mayakan ‘yan tawayen suka zargi shugaba Faustin Archange Touadera da yunkurin tafka magudi a zaben shugabancin kasar Afrika ta Tsakiyan, domin zarcewa kan wa’adi na 2.

A karshen makon da ya gabata ne kuma gwamnatin Touadera ta zargi tsohon shugaba Francois Bozize da shirin jagorantar juyin mulki, bayan hada kai da ‘yan tawaye, wadanda dakarun wanzar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya suka bayyana wargaza yunkurinsu na afkawa Bangui, babban birnin kasar.

Tuni dai Faransa ta aike da jiragen yakinta domin samar da tsaro yayin gudanar zabukan Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.