Isa ga babban shafi
Afrika

Sojin MDD sun karbe garin Bambari daga 'yan tawaye

Dakarun Majalisar Dinkin Duniya sun sake karbe iko da gari na hudu mafi girma a Jamhuriyar Tsakiyar Afrika daga hannun ‘yan tawaye a daidai lokacin da ake shirin gudanar da zaben shugaban kasar.

Wasu daga cikin sojojin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya.
Wasu daga cikin sojojin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya. REUTERS/Adama Diarra
Talla

Mai Magana da Yawun Rundunar Wanzar da Zaman Lafiya ta MINUSMA, Abdoulaziz Fall ya shaida wa manema labarai a birnin Bangui cewa, yanzu haka hankula sun kwanta a garin na Bambari.

Jami’in ya kara da cewa, tuni fararen hula suka fara tururuwar komawa gidajensu da ke garin bayan an yi nasarar fatattakar ‘yan tawayen masu rike da bindigogi.

Wannan na zuwa ne bayan gwamnati ta yi zargin cewa, tsohon shugaban kasar, Francois Bozize na shirin yin juyin mulki tare da hadin guiwar ‘yan tawayen gabanin gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisa a ranar Lahadi mai zuwa.

Tuni kasashen Rasha da Rwanda suka aike da daruruwan sojoji domin agaza wa Jamhuriyar Tsakiyar Afrika bayan gwamnatin kasar ta bukaci tallafin kasashen na ketaren.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.