Isa ga babban shafi
Hakkin dan adam

Faransa ta kama dogarin tsohon shugaban Afrika ta Tsakiya

Jami’an tsaron Faransa sun kama Eric Danboy Bagale, dogarin tsohon shugaban Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya Francois Bozize, bisa tuhumarsa da laifukan take hakkin dan adam.

François Bozizé, tsohon shugaban Afrika ta Tsakiya
François Bozizé, tsohon shugaban Afrika ta Tsakiya Simon Maina/AFP
Talla

A sanarwar da suka fitar jiya asabar, hukumar yakar ta’addaci ta Faransa tace tun a ranar Talata jami’anta suka damke Bagale mai shekaru 41 a gabashin kasar.

Ana dai tuhumar Bagale tsohon dogarin hambararren shugaba Bozize ne da laifukan azabtar da jama’a da kuma jagorantar haddasa barkewar yaki a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya a matsayin shugaban mayakan sa kai na anti-Balaka, a tsakanin shekarar 2007 zuwa 2014.

Yanzu haka dai Bozize da ya koma kasar Afrika ta Tsakiyan daga Uganda, inda ya shafe watanni yana gudun hijira, tun bayan kifar da gwamnatinsa da Michel Djotodia yayi a shekarar 2013.

Yanzu haka dai jam’iyyar adawa ta 'Kwa na Kwa' ta sake baiwa Bozize tikitin yi mata takara a zaben shugabancin kasar dake tafe a watan Disamba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.