An soma taron sasanta rikicin Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya
An soma taron tattaunawa don kawo karshen mummunan rikicin da ya dabaibaye Jamhuriyar Afrika Ta Tsakiya a Khartoum, babban birnin Sudan.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Taron da aka fara a ranar Alhamis, na samun halartar wakilan gwamnati da kuma kungiyoyi 14 da suka dauki makamai.
Taron da ke karkashin jagorancin Tarayyar Afirka, shi ne karo na takwas cikin shekaru shida da kungiyar ta yi tanalalubo mafitar kawo karshen rikicin.
Dubban mutane ne suka mutu tun shekarar 2013, kana mutane miliyan 4 da rabi suka tsere daga gidajensu sakamakon rikicin da ya barke a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiyar.
Gwamnatin Sudan ta ce za a shafe makwanni uku ana gudanar da taron, don samun masalaha mai dorewa.
Rikicin Jamhuriyar Afrika Ta Tsakiya yasamo asali ne a shekarar 2013, lokacin da kungiyar ‘yan tawayen Seleka ta kifar da gwamnatin shugaba Francois Bozize, juyin mulkin da yayi sanadin bullar ‘yan tawayen anti-Balaka, wadanda akasarinsu kiristoci ne.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu