Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Afrika Tsakiya

'Majalisar dinkin duniya ta gaza hukunta dakarunta kan laifukan fyade'

An sake bankado sabbin zarge-zarge na yadda Majalisar dinkin duniya ta gaza daukar matakan da suka dace, kan dakarun wanzar da zaman lafiyar da ta tura zuwa jamhuriyar Afrika ta tsakiya, bayan ta tabbata cewa sun yi wa mata fyade, ciki harda yara kanana.

Wasu daga cikin dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, yayinda suke sintiri a birnin Bangui, babban birnin kasar Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.
Wasu daga cikin dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, yayinda suke sintiri a birnin Bangui, babban birnin kasar Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya. MARCO LONGARI / AFP
Talla

Wata kungiyar fafutuka da ke Birtaniya ta sanar da samun rahotanni har kashi 14, da suka yi cikakken bayani dangane da kararrakin dakarun wanzar da zaman lafiyar, da aka fi sani da MINUSCA, da aka gabatar, ba kuma tare da majalisar ta hukunta su ba.

Dakarun da ake zargi da aikata laifukan fyaden sun fito ne daga kasashen Burundi, Kamaru, Masar, Gabon, Morocco, Nijar, Pakistan, Jamhuriyar Kongo da kuma Zambia

A shekarar 2014, MDD ta aike da dakaru 10,000 zuwa jamhuriyar Afrika ta tsakiya domin maido da zaman lafiya, bayan barkewar rikicin addini da yayi sanadin mutuwar dubban mutane, da raba miliyoyi da gidajensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.