Isa ga babban shafi
Afrika ta Tsakiya

Afrika ta Tsakiya: Mutane 88,000 sun tsere cikin wata daya

Majalisar Dinkin Duniya ta ce sake barkewar tashe tashen hankula a Jamhuriyyar Afrika ta Tsakiya, daga farkon watan Mayu da muke ciki zuwa yanzu, ya tilastawa akalla mutane dubu 88 tserewa daga gidajensu. 

Wasu daga cikin 'yan gudun hijirar da sabon tashin hankali ya raba da gidajensu a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.
Wasu daga cikin 'yan gudun hijirar da sabon tashin hankali ya raba da gidajensu a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya. unhcr.org
Talla

Mai magana da yawun majalisar dinkin duniyar Babar Baloch, ya ce, tashin hankalin ya fi kazanta a kauyukan da ke kan iyakar kasar da Jamhuriyar Congo.

Cikin rahoton da ta fitar a yau Talata hukumar lura da ‘yan gudun hijirar ta majalisar Dinkin Duniyar, ta ce a farkon watan Mayu kadai akalla mutane 68,000 ne suka tsere yankunan da tashe tashen hankulan suka yi kamari a jamhuriyyar Afrika ta tsakiyan, yayinda a cikin makwani biyun da suka gabata kadai wasu 20,000 suka sake tserewa zuwa jamhuriyyar Kongo.

Hakan ya sabbaba karuwar yawan wadanda suka rasa matsugunnasu cikin Jamhuriyar Afrika ta tsakiya zuwa sama da 500,000, yayinda yawan wadanda a yanzu ke gudun hijira a jamhuriyar Congo da suke makwabtaka da ita, ya zarta 120,000.

Wani rahoton hadin gwiwa ta majalisar dinkin duniya da hukumar bada agaji da Red cross suka fitar a ranar 13 ga watan Mayu da muke ciki, ya ce akalla mutane 108 aka yiwa yankan rago, tare da raunata wasu 76, yayin harin da wasu mayakan ‘yan tawaye suka kai a garin Bangassou da ke kan iyakar jamhuriyar Afrika ta tsakiyan da jamhuriyar Congo.

Tun a shekara ta 2013 kasar ta fada cikin tashin hankali, bayan barkewar fada tsakanin mayakan Seleka Musulmi da na Anti Balaka Kristoci, inda suke kokarin kwace ragamar iko da kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.