Isa ga babban shafi
Africa ta Tsakiya

An kashe mutane 100 a kudancin Africa ta Tsakiya

Sama da mutane 100 aka kashe a kudancin kasar Africa ta Tsakiya, sakamakon wani sabon tashin hankali da ya barke, mai alaka da addini da kabilanci.

Mayakan Seleka a Jamhuriyar Afika ta Tsakiya
Mayakan Seleka a Jamhuriyar Afika ta Tsakiya E. Dropsy
Talla

Kakakin sakataren majalisar dinkin duniya, Stephen Dujarric, ya ce zuwa yanzu sabon fadan ya tilastawa fararen hula dubu 8 da 500 tserewa daga muhallansu, baya ga wasu sama da dubu 2 da suka ketara Congo.

Tun a ranar Litinin da ta gabata ne fadan ya kazanta a garin Bria mai nisan kilomita 300 daga birnin Bangassou da ake hako Zinare, lamarin da ya tilastawa mazauna garin akalla 1000 neman mafaka a kusa da hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya.

Rahoton Majalisar ya zo a dai-dai lokacin da kungiyar bada agaji ta Red Cross ta sanar da gano gawarwakin mutane 115, wanda ke dauke da raunukan harbi da bindiga, a garin Bangassou inda ake hako Zinare.

Al’amarin da ke zuwa kwanaki bayan kazamin fadan da aka gwabza a tsakanin kungiyoyin ‘yan tawayen da ke fafutukar kwace iko da birnin na Bangassou, saboda arzikin Zinaren da ya ke da shi.

Sai dai Zuwa yanzu dakarun Majalisar Dinkin Duniya sun kwato muhimman sassan da mayakan ‘yan tawayen suka kwace a kudancin birnin Bangassou a karshen satin da ya gabata.

Rikicin Africa ta Tsakiya dai ya samo asali ne bayanda mayakan Seleka musulmi suka kifar da gwamnatin Francois Bozize, abinda ya jawo hare-haren ramako daga mayakan anti-balaka mabiya kristanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.