Isa ga babban shafi

Mun kai hari barikin Mali ne saboda dauko sojojin hayar Wagner - 'Yan ta'adda

Wata kungiya mai alaka da Al-Qaeda ta dauki alhakin mummunan harin kunar bakin wake da aka kai babbar barikin sojoji dake kusa da babban birnin kasar Mali.

Wasu dakarun sojin hayar kamfanin tsaron Rasha Wagner dake Mali
Wasu dakarun sojin hayar kamfanin tsaron Rasha Wagner dake Mali © @ RFI Mandenkan
Talla

Dama dai sojojin Mali sun zargi mayakan kungiyar Katiba Macina da kai harin na ranar Juma'a da cikin wasu motoci biyu da aka makare da bama-bamai da suka kashe a kalla soja daya a Kati, barikin da shugaban rikon kwaryar kanal Asimi Goita ke ciki.

Majiyoyin suka ce ankai harin ne kusa da gidan shugaban gwamnatin mulkin sojan da kuma ministan tsaronsa.

Cikin sanawar da wani shafi dake bibiyar lamuran ‘yan ta’adda a Mali ya fitar, Kungiyar tace ta kai harin ne saboda sojojin hayan da Mali ta dauko da Rasha don kashe wadanda ba su ji ba ba su gani ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.