Isa ga babban shafi
Mali-Amurka

Amurka ta gargadi Mali game da sojin hayar Wagner na Rasha

Amurka ta gargadi Mali game da amfani sojin hayar kamfanin Wagner na Rasha wajen yakar ayyukan ta’addanci da hare-haren kungiyoyi masu ikirarin jihadi da suka addabi kasar.

Sakataren wajen Amurka Antony Blinken.
Sakataren wajen Amurka Antony Blinken. AP - Olivier Douliery
Talla

Sakataren harkokin wajen Amurkan Antony Blinken ya ce yarjejeniyar kasar ta yammacin Afrika da kamfanin ba komai za ta haifar face sake wargaza tsaron kasashen nahiyar.

Kalaman na Blinken da ke zuwa kwanaki 2 bayan Tarayyar Turai ta bi sahun Amurka wajen sanya takunkumai kan kamfanin na Wagner, ya ce abin takaici ne yadda kasar karkashin mulkin Soji ta yi watsi da bukatar kara mata yawan dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya don magance matsalar tsaron.

Sanarwar gargadin da Blinken ya fitar, ta bayyana kamfanin na Wagner a matsayin wanda ya yi kaurin suna wajen take hakkin dan adam da kuma damalmala matsalolin tsaron da kasa ke fuskanta da zarar ya sanya kafa cikinta.

Sanarwar ta ruwaito Blinken na rokon gwamnatin rikon kwaryar ta Mali da ta yi amfani da miliyoyin kudin da za ta biya sojin hayar na Wagner kan dakarunta na cikin gida don karfafa musu gwiwa wajen yakar ta’addancin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.