Isa ga babban shafi
Faransa-Rasha

Ba zamu amince da girke dakarun Wagner a yankin Sahel ba- Faransa

Faransa ta yi gargadin cewa ba za ta taba amincewa kasar Rasha ta tura sojin hayar kamfanin Wagner zuwa yankin Sahel da Sahara ba. Wannan gargadi dai na kunshe ne a wata sanarwa da aka fitar bayan wani taro da ministocin Faransa da na Rasha suka gudanar yau juma'a a birnin Paris.

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa.
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa. © REUTERS - GONZALO FUENTES
Talla

A lokacin ganawar tsakanin ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian, da ministar tsaron kasar Florence Parly da kuma takwarorinsu na kasar Rasha Sergei Lavrov da Sergei Choigou, Faransa ta fito fili karara inda ta nuna rashin amincewa da duk wani yunkurin tura sojin hayar da kamfanin Wagner zuwa yankin Sahel.

Gargadin na Faransa dai na zuwa a dai dai lokacin da gwamnatin mulkin sojin Mali ke cewa ba ta debe tsammanin gayyato sojin hanyar na Wagner don taimakawa kasar tunkarar matsalolin tsaron da ta ke fama da ita ba.

Sanarwar da Faransa ta fitar ta ce matukar dai aka bai wa sojin hayar damar shiga yankin Sahel, to ba abin da hakan zai haifar face mayar da hannun agogo baya a yunkurin da ake na samar da zaman lafiya a yankin baki dayansa.

A watannin baya-bayan nan dai alaka ta yi matukar tsami tsakanin Faransa da Mali, bayan da sojoji wadanda suka kwaci mulki karkashin jagorancin kanar Assimi Goita suka nuna shawarsu ta gayyato sojin hanya don taimaka masu a yaki ayyukan ta’addanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.