Isa ga babban shafi

Dakarun Wagner za su ci gaba da aiki a Afrika - Rasha

Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergie Lavrov ya ce sojojin hayar kamfanin Wagner, za su ci gaba da aikin tabbatar da tsaro a Mali da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, duk da yunkurin yin tawayen da shugabansu Yevegeny Prigozhin ya yi a karshen mako. 

Shugaban dakarun Wagner tare da baradansa.
Shugaban dakarun Wagner tare da baradansa. via REUTERS - VIDEO OBTAINED BY REUTERS
Talla

 

Rasha ta bayyana matsayar tata ce yayin da ya rage sa’o’i kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya yi zama akan makomar aikin dakarunsa na MINUSMA da ke aikin wanzar da zaman lafiya a Mali. 

A yayin hirarsa da RFI, Oumar Berte, Lauya kuma msananin siyasar kasa da kasa da ke Mali ya ce,

Duk da cewar ya yi wuri a yanke hukunci kan yanayin da ake ciki, dole ne mahukuntan Mali su zabi wanda za su ci gaba da tafiya da shi tsakanin shugaba Putin da kuma Prigozhin da ke jagorantar Wagner. 

Masharhancin ya kara da cewa, "A halin yanzu dai gwamnatin kasar ta Mali na tafiya ne tare da bangarorin biyu, kuma har yanzu babu wani sauyi da aka samu, sai dai dole ta sauya zani idan har ba a samu daidaito tsakanin gwamnatin Rasha da sojojin hayar na Wagner ba."

A takaice dai Mali ba za ta fuskanci wata matsala ba, idan aka dinke barakar Rasha da Wagner, amma fa in haka ba ta samu ba, mahukuntan Mali za su fuskanci yanayin rana zafi inuwa kuna, domin dole su zabi bangare daya, kowane zabi na da kalubalen da zai haifar. Inji shi.

Tuni gwamnatin Rasha ta bayyana cewa, za ta ci gaba da gudanar da bincike kan shugaban na Wagner duk da cewa, fadar Kremlin ta sanar da cimma yarjejeniyar sasantawa da shi kan cewa, za ta janye duk wata tuhuma a kansa, amma da sharadin ya fice zuwa Belarus don samun mafaka.

Kasashen duniya sun ci gaba da zura ido domin ganin yadda za ta kaya tsakanin gwamnatin shugaba Vladimir Putin da shugaban na Wagner wanda ya jagoranci yi wa gwamnati bore, lamarin da ya kusan jefa Rasha cikin yakin basasa mafi muni cikin gomman shekaru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.