Isa ga babban shafi

Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya na shirin gudanar da zaben raba gardama a ranar Lahadi

Masu kada kuri'a a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya za su kada kuri'u a ranar Lahadi kan wani shiri mai cike da cece-kuce na sauya kundin tsarin mulkin kasar, wanda zai bude kofar shiga wa'adi na uku ga shugaba Faustin Archange Touadera.

Kasuwar Birao kenan da ke arewacin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.
Kasuwar Birao kenan da ke arewacin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. © AFP/Alexis Huguet
Talla

Kasar wadda ta kasance daya daga cikin kasashe masu fama da talauci da tashin hankali a duniya, ta shafe fiye da shekaru goma tana fama da rikici da rudanin siyasa.

An fara zaben Touadera ne a shekarar 2016, tare da taimakon Faransa da Majalisar Dinkin Duniya, bayan ta fita daga yakin basasar da ya barke kan kabilanci sakamakon juyin mulki.

Ana ci gaba da tashe tashen hankula har yanzu a kasar, ko da yake Kungiyoyin 'yan tawaye ne ke iko da yankunan kasar da dama, kuma shi kansa Touadera ya ci gaba da kasancewa a kan karagar mulki ne tare da goyon bayan dakarun Rasha.

An sake zaben Touadera a shekara ta 2020 bayan kuri'ar da take cike da zarge-zargen magudi da rashin fitowar jama'a, kasa da daya cikin kashi uku na al'ummar kasar ne suka kada kuri'a, a wancan lokacin, musamman saboda barazana da ake fuskanta a yankunan da 'yan tawaye ke rike da su.

Canjin kundin tsarin mulkin da ake shirin yi zai daga wa'adin mulkin shugaban kasa daga shekaru biyar zuwa bakwai, tare da soke wa'adinsa, domin samun damar sake tsayawa takara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.