Isa ga babban shafi

Daruruwan dakarun Wagner sun isa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Sama da sojojin Wagner 100 ne suka isa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya domin tabbatar da tsaro gabanin zaben raba gardama na ranar 30 ga watan Yuli, kamar yadda wata kungiyar da ke da alaka da kungiyar sa-kai ta Rasha ta sanar.

Dakarun Wagner kenan a arewacin Mali.
Dakarun Wagner kenan a arewacin Mali. AP
Talla

Dakarun na Rasha za su ci gaba da taimaka wa sojojin Afirka ta Tsakiya da jami'an tsaro wajen samar da tsaro, a zaben raba gardama na kundin tsarin mulkin da aka shirya gudanarwa a ranar 30 ga watan Yuli," in ji sanarwar.

A farkon watan Yuli, wasu majiyoyin kasashen waje da dama sun yi ikirarin cewa wasu sojojin haya na Wagner da ba a san adadinsu ba suna barin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, bayanan da gwamnati ta musanta.

Matsayin kamfani mai zaman kansa da kuma ci gaba da gudanar da ayyukansa ba shi da tabbas tun bayan dambarwar da ta kunno kai a Rasha a watan Yuni.

Amma samun guraben zama da ta yi a kasashen waje, musamman a Syria da wasu kasashen Afirka irin su Sudan , Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Mali an gaza samo amsa a kai.

Da aka sanar da kawo karshen tuhumar da kamfanin ke fuskanta, gwamnatin Bangui ta tabbatar da cewa ayyukan Wagner za su ci gaba da wanzuwa a kasarta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.