Isa ga babban shafi

Amurka ta zargi Rasha da amfani da Wagner wajen samun kudin yaki a Ukraine

Amurka ta yi zargin cewa Rasha na amfani da Sojojin hayar kamfanin Wagner mallakinta wajen tatsar kudaden da ke daukar nauyin yakinta a Ukraine daga kasashen Afrika, ta hanyar fakewa da sunan basu tsaro ko kuma yakar ta’addancin da kasashen kef ama da shi.

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Linda Thomas-Greenfield.
Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Linda Thomas-Greenfield. LUSA - ELTON MONTEIRO
Talla

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Linda Thomas-Greenfield ta yi zargin cewa, ko shakka babu kasashen Afrika na biyan kamfanin Wagner makudan kudade akan ayyukan da ya ke yi a kasashen nahiyar da sunan yaki da matsalolin tsaro.

A jawabin da ta gabatar gaban zaman kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, Thomas-Greenfield ta ce Rasha na amfani da sojojin na Wagner wajen fasakwaurin albarkatun karkashin kasa zuwa sassan Duniya wanda da shi ne take samun tarin kudaden shiga.

A cewar jakadar da kudin ma’adanan da Rasha ke dauka daga Afrika ne ta ke biyan sojojin hayar na kamfanin Wagner wadanda ke yake-yake a gabas ta tsakiya da Afrika da kuma yanzu haka mamayar kasar a Ukraine.

Duk da cewa gwamnatin Rasha na ci gaba da nesanta kanta da kamfanin tsaron na Wagner amma wasu majiyoyi na cewa kamfanin mallakin shugaba Vladimir Putin ne.

Dakarun na Wagner dai sun shiga Libya a 2016 inda suke taimakawa tsagin Khalifa Haftar yayinda aka gansu a jamhuriyyar Afrika ta tsakiya cikin shekarar 2017, baya kasancewarsu a Sudan inda suke tsaron mahakun zinare sai kuma shigarsu Syria da ake ganin shi ya hana faduwar gwamnatin Bashar al-Assad yayinda a baya-bayan nan suka isa Mali don magance matsalar tsaron da kasar ke fama da ita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.