Amurka tace Mali na biyan Wagner Dala miliyan 10 kowane wata
Kasar Amurka tayi zargin cewar gwamnatin sojin Mali na biyan kamfanin sojojin haya Rasha da ake kira Wagner Dala miliyan 10 kowanne wata domin gudanar da aikin tsaro a kasar.
Wallafawa ranar:
Kwamandan sojin Amurka dake kula da nahiyar Afirka, Janar Stephen Townsend ya bayyana haka, inda yake cewa sojojin hayar na kamfanin Wagner na goyawa sojin Mali baya da sunan yaki da ‘Yan ta’adda a cikin kasar.Janar Townsend ya bayyana zaman kamfanin Wagner a cikin Mali a matsayin abin takaici wanda ba zai iya samarwa kasar da tsaron da take bukata ba.
Kwamandan yace suna da yakinin cewar kamfanin na karbar Dala miliyan 10 daga gwamnatin kasar kowanne wata, kuma ya na zaton za’a ayi amfani da ma’adinan kasar da suka hada da zinare ne wajen biyan su.
Kasar Mali ta fada cikin tashin hankali tun daga shekarar 2012 inda ayyukan ‘Yan bindiga suka jefa kasar cikin mummunar yanayi, abinda ya yadu zuwa kasashen Nijar da Burkina Faso.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu