Isa ga babban shafi
Mali - Faransa

Mali ta zargi Faransa da marawa wasu shugabannin juyin mulki baya

Ministan Harkokin wajen Mali ya bayyana cewar tsamin dangantakar dake tsakanin su da Faransa ya biyo bayan bijirewa manufofin kasar ne, sabanin jinkirta zaben shugaban kasar da ake matsa musu lamba akai.

Ministan harkokin wajen Mali Abdoulaye Diop.
Ministan harkokin wajen Mali Abdoulaye Diop. © RFI/France24
Talla

Ministan Abdoulaye Diop ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabi ga Yan kasar Mali dake zama a Brussels, inda ya zargi Faransa da nuna son kai wajen sukar mulkin soji.

Diop yace Faransa wadda tace tana kare mulkin dimokiradiya taje wasu kasashe inda ta dora shugabanni da suka yi juyin mulkin na soji ta kuma jinjina musu.

Dangantaka tsakanin Mali da Faransa wadda ta yiwa kasar mulkin mallaka tayi kamari tun bayan juyin mulkin da soji suka yi a watan Agustan shekarar 2020.

Faransa na da dubban sojoji a kasar Mali wadanda ke rundunar yaki da Yan ta’adda a yankin Sahel.

Ana ci gaba da tankiya a kasar tun bayan takunkumin da ECOWAS ta dorawa Mali na karya tattalin arziki sakamakon juyin mulkin wanda ya samu goyan bayan Faransa da Amurka da kungiyar kasashen Turai.

Ministan harkokin wajen Faransa Jean Yves Le Drian ya bayyana gwamnatin sojin Mali a matsayin haramtacciya, inda ya zarge ta da kaucewa gudanar da zabe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.