Isa ga babban shafi

Afrika ta tsakiya ta gano masu hannu a harin da ya raunata wakilin Rasha

Babban mai gabatar da kara na gwamnatin Jamhuriyar Afirka ta tsakiya ya ce wani harin bam da aka kai kasar makon da ya gabata da ya raunata wani wakilin Rasha a Bangui daga Togo ya samo asali kuma tuni suka gano wanda ya yi aika-aikar.

Wasu Sojojin Jamhuriyar Afrika ta tsakiya.
Wasu Sojojin Jamhuriyar Afrika ta tsakiya. AFP PHOTO / MUJAHID SAFODIEN
Talla

Tun a ranar Juma’ar da ta gabata masu gabatar da kara a Bangui babban birnin Afirka ta Tsakiya suka sanar da bude bincike bayan da Rasha ta tabbatar da cewa daya daga cikin wakilanta ya samu rauni sakamakon fashewar wani abu a birnin.

A ranar Asabar ofishin jakadancin Rasha da ke Bangui ya ce jami’in na cikin mawuyacin hali kwance a asibiti amma baya cikin hadari.

Tuni shugaban kamfanin bada sojojin hayar Wagner ta kasar Rasha, Yevgeny Prigozhin, ya zargi Faransa da kai harin, kuma nan take mahukunta a Paris suka musanta.

Gwamnan Afirka ta Tsakiya ta yi tir da wannan hari da kakkausar murya, ta na mai cewa wani yankuri ne na bata alaka mai karfi da ke tsakaninta da Rasha.

Mai gabatar da kara na gwamnatin Afirka ta Tsakiya Benoit Narcisse Foukpio da ya alakanta harin da ta’addanci, ya ce binciken farko ya gano cewa wani kunshi ne dauke da wani abun fashewa aka aika daga Lome babban birin Togo, kuma kamfanin aike da sakonni na DHL ne ya shigo da shi kasar ta jirgin saman kamfanin Kenyan Airways.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.