Isa ga babban shafi

MSF ta zargi Sojin Afrika ta tsakiya da kisan jami'inta guda

Kungiyar likitocin kasa da kasa ta Doctors without borders ko kuma MSF ta ce wani soja a Jamhuriyar Afrika ta tsakiya ya harbe daya daga cikin ma’aikatanta har lahira a kasar mai fama da rikici tsawon lokaci.

Wasu jami'an kungiyar MSF.
Wasu jami'an kungiyar MSF. © Lou Roméo / RFI
Talla

A cikin wata sanarwa da kungiyar ta MSF ta fitar a wannan Talata ne, ta ce jami’inta da ke aikin rarraba magunguna mai suna Mahamat Ahamat, mai shekaru 46, ya gamu da ajalinsa ranar Asabar a Moyenne – Sidi wani gari mai tazarar kilomita 500 daga babban birnin kasar Bangui da ke kusa da iyakar kasar Chadi.

Kungiyar da ta ce ma’aikacinta ya gamu da ajalinsa na bayan shan ruwan harsasai har guda uku, ta yi Allah wadai da abin da ta kira "kisan gilla " tare da kira ga hukumomi da su gudanar da bincike.

Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da ke makwabaka da Kasashen Chadi da Kamaru na daga cikin kasashe mafi talauci a duniya duk da dunbin albarkatun kasa da Allah ya yi mata, yayin da ta fada cikin tashin hankali tun bayan barkewar yakin basasa a shekarar 2013.

Duk da cewa an dan samu lafawar rikici tun a shekarar 2018, amma har yanzu yawancin sassan kasar na cikin damuwa matuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.