Isa ga babban shafi

MDD ta yaba da matakin kawo karshen hukuncin kisa a Afrika ta tsakiya

Hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta yaba da matakin da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya na kawo karshen yanke hukuncin kisa a kasar, wanda ke zuwa bayan tafka muhawara kan kudirin na shugaba Faustin-Archange Touadéra a gaban Majalisar dokokin kasar.

A ranar 'yancin Afrika ne shugaban kasar ya sha alwashin kawo karshen zartas da hukuncin kisa a sassan Jamhuriyar Afrika ta tsakiya.
A ranar 'yancin Afrika ne shugaban kasar ya sha alwashin kawo karshen zartas da hukuncin kisa a sassan Jamhuriyar Afrika ta tsakiya. AP - Hossein Esmaeli
Talla

Tun shekarar 1981 ba a aiwatar da hukuncin kisa a Jamhuriyar Afirka ta tsakiya ba, kuma a ranar Juma'ar da ta gabata 'yan majalisar suka amince da sabuwar dokar da ta haramta yanke hukuncin kisa.

Babbar jami'ar kare hakkin bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya, Michelle Bachelet a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce, hukuncin kisa bai dace da ainihin ka'idojin 'yancin dan adam ba.

Tun a shekara ta 2013, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, wadda ita ce kasa ta biyu mafi karancin ci gaba a duniya a cewar Majalisar Dinkin Duniya, ta fada cikin yakin basasa.

Za ta zama kasa ta 24 a Afirka da ta soke hukuncin kisa, inda a yanzu haka kimanin kasashe 170 ne suka soke hukuncin kisa a cikin doka ya zuwa yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.