'Yan majalisar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun soke hukuncin kisa
'Yan majalisar dokokin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun kada kuri'ar amincewa da soke hukuncin kisa, matakin da suka aiwatar a ranar Juma'ar da ta gabata.
Wallafawa ranar:
A halin da ake ciki, kallo ya koma ga shugaba Faustin-Archange Touadera, wanda dole sai ya sanya hannu kan sabuwar dokar ta soke hukuncin kisa a kasar kafin ta tabbata.
Kasar dai ta bi sahun Chadi a shekarar 2020 da Saliyo a shekarar bara wajen kawo karshen hukuncin kisa a nahiyar Afirka a shekarun baya bayan nan.
Hukuncin kisa na karshe da aka zartas a Jamhuriyar Afirka ta tsakiya ya kasance a shekarar 1981.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu