Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Shugaban Afrika ta Tsakiya ya ayyana tsagaita wuta a rikici da 'yan tawaye

Shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Faustin-Archange Touadera ya ayyana tsagaita wuta a yakin  da gwamnati ta dade tana yi da 'yan tawaye, yana mai cewa dukkan manyan kungiyoyin da ke dauke da makamai sun amince su ajiye makamansu face biyu da suka yi watsi da batun.

Shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Faustin-Archange Touadéra, 17/09/21.
Shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Faustin-Archange Touadéra, 17/09/21. © Carol Valade / RFI
Talla

Kasar ta fada cikin yakin basasa na zubar da jini bayan juyin mulkin a shekarar 2013, kuma duk da yanayin tashin hankalin ya ragu matuka cikin shekaru uku da suka gabata, to amma har yanzu kungiyoyin da ke dauke da makamai na iko da manyan yankunan kasar.

Touadera dake sanar da matakin maraicen jiya ta gidan rediyon kasar yace " sun kawo karshen ayyukan soji da ke fafatwa da ‘yan tawaye a fadin kasar, matakin da ya soma aiki tun a daren jiya.

Shugaban yace ya dauki matakin ne domin Fifita tattaunawa da kungiyoyin masu dauke da makamai don samar da zaman lafiya mai dorewa a jamhuriyar Afirka ta tsakiya wanda ta shafe shekaru takwas tana fama da rikici.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.