Isa ga babban shafi
Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya

Mamayar 'yan tawaye ya tilasta 'yan Afrika ta tsakiya dubu 60 barin muhallansu

Hukumar kula da ‘yan cirani ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce yanzu haka akwai dubunnan al’ummar Afrika ta tsakiya da suka tsere daga muhallansu saboda tsanantar rikici a kasar.

Ko a makon jiya sai da ‘yan tawayen suka yi yunkurin kwace iko da babban birnin kasar Bangui dai dai lokacin da yunwa ke ci gaba da tsananta.
Ko a makon jiya sai da ‘yan tawayen suka yi yunkurin kwace iko da babban birnin kasar Bangui dai dai lokacin da yunwa ke ci gaba da tsananta. REUTERS/Stefano Rellandini
Talla

Wani rahoto da hukumar ta fitar ta ce dubunnan mutane daga kananun kauyuka sun sulale a boye tare da tserewa daga muhallan na su bayanda dakarun ‘yan tawayen kasar suka kwace iko da kauyukansu.

Rikici tsakanin ‘yan tawayen da dakarun gwamnati baya ga na Majalisar Dinkin Duniya da kuma na Rasha da Rwanda da ke taimakawa Jamhuriyyar Afrika ta tsakiyar na ci gaba da tsananta ne tun cikin watan Disamban bara yayinda ya sake ta’azzara bayan zaben kasar da ya baiwa shugaba mai ci nasara.

Rahoton Majalisar Dinkin Duniyar ya ce yanzu haka akwai jumullar ‘yan kasar dubu 60 da suka bar muhallansu musamman daga yankunan karkara inda ‘yan tawayen ke da karfi, yayinda wasu akalla dubu 5 suka samu mafaka a makwabciyar kasar Kamaru.

Rahotanni sun ce yanzu haka dakarun kasar na aikin bayar da tsaro ne akan manyan iyakokin da suka hada shiyyoyin kasar don dakile barazanar bazuwar ‘yan tawayen zuwa sauran sassa.

Ko a makon jiya sai da ‘yan tawayen suka yi yunkurin kwace iko da babban birnin kasar Bangui dai dai lokacin da yunwa ke ci gaba da tsananta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.