Isa ga babban shafi

Rikicin Afrika ta Tsakiya ya janyo karancin abinci a Bangui

Sojan Gwamnatin Afirka ta tsakiya dake samun tallafin sojan hayar kasar Rasha da na Rwanda na ci gaba da fafatawa da yan tawaye, wannan ne ya kawo cikas ga zirga zirgar yan kasuwa dake shigar da kaya Bangui daga kasar Kamaru.

Dawowar 'yan gudun hijirar Afrika ta Tsakiya daga Congo.
Dawowar 'yan gudun hijirar Afrika ta Tsakiya daga Congo. Charlotte Cosset/RFI
Talla

A yanzu kayan abinci da na masarufin yau da kullum sun daina shiga garin Bangui sabili da cewa hanyar Kamaru ce daya tilo ake shigar da kaya a baya bayan nan.

Bisa dukan alamu dai ana tsoron yiwuwar barkewar yunwa a wannan gari, kuma domin magance wannan matsala Firaminsitan kasar ya bayyana cewa daga ranar Talata sojoji zasu dinga rakiyar motocin abinci har cikin babban birnin Bangui daga kasar kamaru.

Yan tawaye sun kai hari ranar asabar a garin Bouar dake kilometa 340 da babban birnin kasar inji dakarun majalisar dinkin duniya na Munisca, kuma jiragen yakin Faransa sun gudanar da sintiri ta sama don yin kashedi ga yan tawayen.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron yayi Allah wadai da yunkurin yan tawayen na neman tada zaune tsaye da kawo cikas ga zababiyar gwamnati, sannan ya bukaci masu rikicin su tattauna.

Garin Bouar mai mutane dubu 40, shine birni na biyar a kasar dake kan hanya mai mihimmanci dake hada kasar ta Afirka ta tsakiya da Kamaru, wacce ta nan ne ake kai kayan abinci zuwa Bangui.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.